Da tsakar daren ranar Asabar ce Iran ta ƙaddamar da hare-haren a Isra’ila, inda ta harba jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami fiye da 200.
Iran ta kai waɗannan hare-haren ramuwar gayya ne bayan Isra’ila ta kai hari a ofishin jakadancinta da ke Syria, inda ta kashe zaratan sojojinta bakwai ciki har da masu muƙamin janar.
Jirage marasa matuƙa da makamai masu linzamin da Iran ta harba su ne karon farko da take kai hari Isra’ila kai-tsaye daga cikin ƙasarta.
Waɗannan hare-hare sun jawo fargaba game da yiwuwar ramuwa daga Isra’ila kan Iran lamarin da zai ƙara zaman ɗar-ɗar ɗin da ake yi a yankin Gabas ta Tsakiya.
Kafafen watsa labarai sun ruwaito cewa wasu daga cikin makaman da Iran ta harba sun sauka a filin jirgin saman Ramon da ke yankin Negev na Isra’ila.
“Makamai masu linzami samfurin Kheibar sun yi nasarar sauka a sansanin jiragen sama mafi muhimmanci na Negev,” kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Iran IRNA ya ruwaito.
DUBA NAN: Gwamnan Kano Ya Bukaci EFCC Ta Cigaba Da Binciken Dala
Negev yana mai ƙarawa da cewa “hotuna da bayanai sun nuna cewa harin ya yi wa wurin
gagarumar ɓarna.”
A wani labarin na daban falasdinawa sun fara komawa gidajensu da yaki ya rugurguza a Birnin Khan Younis da ke gabashin Gaza bayan da dakarun Isra’ila suka janye daga yankin.
Farmakin da sojojin Isra’ila suka kai ta kasa ya dagargaza gine-ginen yankin.
Ministan tsaron Isra’ila ya ce sojojin sun bar yankin ne domin sake dauro sabuwar damarar yakar Hamas a Khan Younis din da Rafah, inda Falasdinawa sama da miliyan ke gudun hijira.