Kafar yada labaran yahudawan sahyuniya ta tabbatar da cewa an harbo wani jirgin mara matuki mallakar wannan gwamnati a yankunan da aka mamaye
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na – ABNA – ya habarta maku cewa: Majiyoyin yada labarai sun rawaito cewa an harbo wani jirgin yakin sahyoniya mara matuki a yankin “Maalot Tarshiha” da ke arewacin kasar Falasdinu da ta mamaye.
A cewar wannan rahoto, kafar yada labaran yahudawan sahyuniya ta tabbatar da cewa an harbo wani jirgin mara matuki mallakar wannan gwamnati a yankunan da aka mamaye.
A wani labarin na daban taron ganawar wasu gungu daga cikin shuwagabannin Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya na kasar Iraki;
Ayatullah Ramezani: Ya Kamata Masu Tabligi Su Ba Da Kulawa Ta Musamman Ga Sabbin Tsatso Zamani Da Matasa
Babban Sakatare Janar na Majalisar Ahlul-Baiti (AS) ya bayyana cewa: Ya kamata masu Tabligi su san irin ladubba da jawabai da za su yi mu’amala da masu sauraro da shi; Game da wannan, ya kamata a horar da mai wa’azi yadda zai bayar da amsoshi ga tambayoyin da ake da shubuha akansu.
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na – ABNA – ya habarta maku cewa: tawagar jagororin majalisar Ahlul-Bait (AS) ta duniya a kasar Iraki, wadanda suke sansanin horo a birnin Qum, sun gana da Ayatullah Reza Ramezani, Babban sakataren majalissar Ahlul Baiti (a.s) kafin azahar din jiya – Laraba 3 ga watan Aban 1402.
Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya a wannan taro da yake maraba da baki, ya bayyana irin yadda Isar da addini yake da muhimmanci da cewa: A yau kula da hanyoyin isar da sakon addini daban-daban, da kayan aikin isarwa, da masu sauraron wa’azi na da matukar muhimmanci ci gaban duniya.
Yayin da yake jaddada zamanantar da masu wa’azin tabligi da hanyoyin wa’azi, ya ce: Aikin masu Tabligi ya yi nauyi a yau, kuma Majalisar Ahlul-baiti (A.S) na da kyakykyawan damar wa’azi a Iraki ta fuskar yawa da inganci.
Yayin da yake jawabi ga shugabannin Majalisar Ahlul-Baiti (AS) na kasar Iraki, ya ce: Wajibi ne a hada littafin da ke dauke da bayanan yadda ake tabligi ta yadda za a shigar da fasahar isar da sako a cikinsa.
Ayatullah Ramezani ya kara da cewa: Ya kamata ‘yan tabligi su san irin ladubba da jawabai da za su yi mu’amala da masu sauraro. Game da wannan, ya kamata a horar da mai wa’azi yadda zai amsa tambayoyi da shubuhohi.
A matsayin shawara ga masu tabiligi na Iraqi, ya ce: Ƙirƙiri tashar wa’azin tabligi ta kai da kai ke bantacciya gareku a cikin sararin samaniya kafofin sadarwa kuma ku haɗa muhimman sunaye da batutuwa da munasabobi a lokuta daban-daban a cikinsa. Misali, a tsakiyar Sha’aban, a yi magana a kan Mahadi da karkacewar da take faruwa a wannan fage.
Source ABNA