Bayan yakin kwanaki goma sha daya da aka gudanar tsakanin falasdinawa da sojojin haramtacciyar kasar isra’ila, wanda ya sabbaba gwamnatin haramtacciyar kasar isra’ilan ta nemi ayi sulhu, amma sai dai a daren jiya 21 ga watan augustan 2021, haramtacciyar kasar isra’ilan ta kaddamar da wani sabon harin kan mai uwa da wani a yankin gaza dake kasar falasdinu.
Tashar talabijin ta Al-alam ta rawaito cewa an jiyo ruwan rokoki na sauka a birnin na gaza wanda mafi yawancin mazauna yankin raunanan falasadinawa ne marasa dauke da makami.
Abinda mutane suka tabbatar dai shine kungiyar neman yancin falasdinu ta Hamas ba zata bar wannan lamari ya wuce hakanan ba tare da sun dauki fansa bisa wannan babban laifin da yahudawan isra’ilan suka tafka kan raunanan farar hula ba.
A wanki bangaren kuma a kalla falasdinawa arba’in da daya ne suka raunata sakamakon harin da sojojin haramtacciyar kasar isra’ila suka kai a kan wani jerin gwanon lumana da falasdinawan suka gudanar a gabashin gaza.
Tashar Al-alam ta rawaito cewa sojojin haramtacciyar kasar isra’ila sun hari masu zanga zangar lumanar ne inda suka dingi ruwan wuta.
Ba sabon abu bane ba dai sojojin haramtacciyar kasar isara’ilan su tari raunanan falasdinawa, fararen hula wadanda basu dauke da makami su dingi harbin su wanda hakan kan sabbaba da dama suji rauni wasu kuma sukan rasa rayukan su sakamakon hari haren ta’addancin na yahudawan sahayoniya a kan falasdinawan.
Ana dai jiran a ga matakin da kungiyar neman ‘yancin falasdinawa ta Hamas zata dauka bisa wannan lamari amma da dama daga cikin falasdinawan a firar su da tashar yada labarai ta Al-alam sun tabbatar da cewa zasu cigaba da fuskantar yahudawan sahayoniya har su rasa rayukan su amma ba zasu taba mika wuya da gwamnatin yahudawa ta haramtacciyar kasar isra’ila ba.
Kasashen larabawa musulmi dai irin su saudiyya da hadaddiyar daular larabawa sune ya kamata su zama gatan raunanan falasdinawa amma sun kame baki sunyi shiru sai dai falasdinawan sukan samu daukin da ba’a rasa ba daga jamhuriyar muslunci ta Iran.