Haramtacciyar isra’ila na cigaba da rusa gidaje da ofishoshin mutanen Falasdinu.
Abin yanzu ya shafi ofishohin gidajen jaridar AlJazeera da AP Kasar Isra’ila ta kai hari gidan benen da ofishin gidan jaridar AlJazeera, AP da wasu kamfanonin jaridar ke ciki a birnin Gaza, kasar Falasdin.
A bidiyon da Alarabiya ta dauka, an ga yadda makami mai linzami da Isra’ila ta harba ya rusa ginin har kasa. Mai ginin benen, Jawwad Mahdi, ya bayyana cewa hukumar Sojin Haramtacciyar kasar Isra’ila ta kirashi cewa za’a kaiwa gidansa hari.
Ya bayyana cewa an fada masa ya sanar da wadanda ke cikin ginin su tattara inasu-inasu su bari cikin awa guda.
A bangare guda, akalla Falasdinawa 139 ne suka rasa rayukansu – ciki akwai kananan yara 40 – a hare-haren da Isra’ila ke kaiwa kuma kimanin mutum 1000 sun jigata suna jinya.
Haramtacciyar Isra’ila ta cigaba da ruwan rokoki kan yankin Gaza kuma ta fara tura Sojojin kasa da motocin yaki cikin Falasdin.
A Arewacin Gaza, Bier Hanoun da Jabalya, na cikin wuraren da Isra’ila ke cigaba da budewa wuta. Hakazalika a gabashin Gaza inda aka yi ruwan bama-bamai a Shuna’iah.
A wani labarin na daban hare-haren da Isra’ila ke kai wa a yankin Zirin Gaza ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa 40 a yau Lahadi, wanda shine adadi mafi muni na wadanda suka mutu a rana guda a kai- ruwa -rana da aka shafe kusan mako guda ana yi, a yayin da kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ke gudanar da taro a kan rikicin da ke ci gaba da ta’azzara.
Yakin wanda shine mafi muni tun bayan shekarar 2014, wanda ya tashi sakamakon rikicin da ya auku a birnin Kudus, ya haddasa musayar wuta daga bangarorin da ba sa ga- maciji da juna, inda yanzu wadanda suka mutu suka kai 181 a yankin Gaza tun daga ranar Litinin, yayin da 10 suka halaka a bangaren Yahudawa, kamar yadda hukumomi suka sanar.
A Gaza, tawagogin ma’aikatan aikin agaji su na aiki tukuru wajen ciro gawarwakin mutane a baraguzan gine –gine da suka ruguje, a yayin da dangi da abokai ke kuka cikin makoki.
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana takaici da yadda lamarin ke shafar akasari fararen hula, da kuma yadda Isra’ila ke kai hare -hare ba kakkautawa