Sayyida ma’asuma wacce diya ce ga Imam Musal Kazeem (S.a), Imami na bakwai a mazhabar iyalan gidan annabta, kuma kanwa ce ga Imam Ali Bn Musa Arridah (S.a) yanzu haka haramin ta uyana birnin Qom dake jamhuriyar musulunci ta Iran.
Tarihi ya tabbatar da cewa bayan hijirar da yayan ta Imam Ali Arridha (S.a) yayi daga madina zuwa khurasan (Mashhad), sayyiuda ma’asuma ta shirya bin wannan yaya nata.
Sayyida ma’asuma ta kama hanya tun daga madina inda ta dauka wannan tafiya mai matukar wahala duk dai domin ta isa ga yayan ta.
A hanya kafin ta isa birnin Qom wanda yana hanyar khurasan (Mashhad) ne aka samu wasu makiya Allah ta’ala suka kaima ayarin ta hari inda a garin haka suka sabbaba mata rashin lafiya wacce ta cigaba da tafiya har ta isa birnin Qom a halin rashin lafiya.
A birinin Qom ne sayyida ma’asuma (S.a) tayi shahada kuma an binne ta a birnin na Qom sa’annan har yanzu haramin ta yana nan a birnin Qom kuma a kowacce rana yana samun ziyartar al’ummomi daga sassan duniya daban daban domin neman albarka gami da neman biyan bukata wajen Allah ta’ala ta hanyar yin tawassuli da sayyida ma’asuma (S.a).
Tarihi ya tabbatar da cewa sayyida ma’asuma babbar malama ce domin tana karantar da dalibai ba adadi wannan yasa tayi shuhura ta bangaren ilimi da tsoron Allah gami kyawawan halaye.
Yana da kyau matan mu dama mazan su dauki darussa daga rayuwar wannan babbar baiwar Allah wacce tarihi ya tabbatar da cewa ta ciri tuta ta kowanne bangare na nagarta da halayen kwarai.
Abin takaici ba kowa ne ya san da tarihin sayyida ma’asuma ba balle ayi maganar daukar darussa daga rayuwar ta mai albarka.
A yanzu haka haramin sayyida ma’asuma yana birnin Qom yayin da na yayan ta Imam Ridah (S.a) yake birnin mashahd duk a cikin kasar Iran.