Har ila yau, alƙawuran Bin Salman ba su cika ba.
Har ila yau Bincike ya nuna a watan da yagabata kasuwancin da ba na mai ba yayi karanci sosai, sobada raguwar siyan sababbin kaya, hakan yana nuni ga raguwar mabukatan kayan ne(Customers).
Ƙididdigar masana’antu ta fadi zuwa 58.1 a watan da ya gabata daga 61 a watan Disamba kuma ya ci gaba da karuwa, Yawan siye siyen(odar) sabbin kaya a watan da ya gabata daga 68.3 zuwa 60.5 a watan december ya ragu, wanda hakan ya nuni raguwar mabukata(Customer).
Raguwar oder sabbin kaya yakan yawaita abokan gasa a bangaren kasuwanci da kuma yawan rage oder,Faduwa ta hudu a wata 6 da suka wuce, hakan ana danganta shine da raguwar mabukata (Customer’s) da kuma yanayin faduwar kasuwanci.
domin samin labarai na gaba👇
Binciken na nuna cewa farashin sayayya ya karu a cikin sauri tun daga watan Mayun 2012, wanda wasu masana suna ikrarin cewa: tsadar sufuri da ke da alaƙa da Tekun Bahar Maliya, da kuma ƙarin farashin kayayyaki da haɗarin samar da kayayyaki shine yajawo wannan hakan.
Bisa ga rahoton Reuters, Naif Al-Ghaith, babban masanin tattalin arziki na bankin Riyadh, ya bayyana cewa, tattalin arzikin da ba na man fetur ba ya ci gaba da bunkasa duk da kalubalen da ke tattare da tsadar kayayyaki da kudaden ruwa.
Wannan raunin ba iya tattalin arzikin kayayyakin saudiya kawai ya taba ba, bugu da kari ma ya hada har da man fetur din wannan kasar.
A watan Oktoban da ya gabata, asusun ba da lamuni na duniya IMF ya yi hasashen cewa, karuwar GDP na kasar Saudiyya, wanda ya ragu matuka a shekarar 2023, sakamakon raguwar farashin mai da rage yawan hakowa, zai kai kashi hudu cikin dari a shekarar 2024.
A cikin rahoton na Oktoba, wannan mai ba da lamuni na duniya ya kiyasta karuwar tattalin arzikin kasar Saudiyya a shekarar 2023 da kashi 0.8%, amma a sabon rahotonsa, ya rage hasashen ci gaban tattalin arzikin kasar ta Saudiyya sosai, kuma a yanzu an yi kiyasin GDP na kasar ya ragu. da 1.1%.
Gwamnatin Saudiyya ta kiyasta karuwar GDP a shekarar 2023 zuwa kashi 0.03%, kuma har yanzu ba a buga kididdigar hukuma ba.
A fannin yawon bude ido, maimakon aiwatar da ayyukan yawon bude ido da saka hannun jari a wadannan ayyuka, Mohammad Bin Salman ya koma kawo yan kwallon kafa masu tsada da ’yan wasa daban-daban daga kasashen Larabawa da ma duniya baki daya, wanda kowannensu ya ci masa biliyoyin daloli.
A fagen samar da ayyukan yi kuwa, ayyukan da Bin Salman ke da’awar sun samar da guraben aikin yi ga ‘yan kasashen waje musamman ma’aikatan fasaha na kasashen yamma, da su zo Saudiyya su tabbatar da tsare-tsaren Bin Salman na hangen nesa da nisa, maimakon samar da ayyukan yi ga al’ummar Saudiyya.
Sedai wannan tsare-tsaren da bin sulaima ke burin aiwatarwa ya dan dakata saboda rashin isasshen kudi.
Abu mafi muhimmanci shi ne rashin cikar kowanne daga cikin wadannan tsare-tsaren da Bin Salman yayi ya haifar da asarar kudade da dama, wanda ya kamata a biya shi ta hanyar karbar karin haraji daga mutanen Saudiyya.