Hanifa Abubakar; Kotu ta umarci a saki Jamila matar Abdulmalik Tanko da ake zargi da kisan yarinyar.
Kotun majistire da ke Jihar Kano ta ba da umarnin a saki Jamila matar Abdulmalik Tanko, wanda ake zargi da sacewa tare da kaisan Hanifa Abubakar mai shekara biyar a birnin na Kano da ke arewacin Najeriya.
Da ma can ana zargin Jamila ne da laifin haɗa baki wajen yin garkuwa da Hanifa da kuma kashe ta, zargin da matar ta musanta ranar Alhamis lokacin da ta bayyana a kotun.
Mai magana da yawun kotunan Kano, Baba Jibo Ibrahim, ya faɗa wa BBC Hausa cewa kotun ta ba da umarnin a sake ta ne bayan ta yi nasarar wanke kanta daga zarge-zargen a gaban kotu.
Ya ƙara da cewa masu shigar da ƙara a ma’aikatar shari’a ta Kano sun amince su yi amfani da ita a matsayin shaida a kan mijinta Abdulmalik, inda za ta sake komawa kotun don bayyana abubuwan da ta sani game da wanda ake zargin.
Abin da Jamila ta faɗa wa kotu
Da take amsa tambayoyi daga lauyan gwamnati Barista Musa Lawan, Jamila ta ce mijinta ya kawo mata yarinya ta tambaye shi ina iyayenta sai ya ce da ita uwar yarinyar ta sami aiki a Saudiyya, kuma ta tafi Abuja don cike wasu takardu.
“Amma har yamma na ga bai mayar da ita gida ba sai nake tambayarsa yaushe mahaifiyar yarinyar za ta dawo gida, kuma me ya sa har yanzu ba ta kira shi ba?
“Sai ya ce ba ta kira ba, daga baya sai ya ce sun yi magana da mahaifiyar yarinyar ta ce akwai layi ba za ta dawo ba a ranar ba,” in ji Jamila.
Ta ci gaba da bayyana wa kotu cewa bayan kwana biyu sai ya sake ce wa mata uwar yarinyar ta taho amma wani uzuri ya tsayar da ita a hanya, daga baya da ta sake tambayarsa, sai ya ce ta daina tambayarsa.
Matar Abdulmalik ta ce ta kai ga sanin sunan yarinyar ne a tsawon kwanakin farko da kai Hanifa gidan, a lokacin da take kuka, ita kuma ta rarrasheta ta haɗa ta da ‘ya’yanta biyu don yin wasa.
Ta shaida wa kotu cewa yarinyar da ke jikin wani hoto da kotu ta yi wa laƙabi da hujja ta 5 lallai Hanifa Abubakar ce.
Sannan ta ce bayan kwana uku ta sake yi wa mijin nata Abdulmalik magana ya ce kudin mahaifiyar yarinyar ne ya ƙare tana Kaduna.
Amma saboda yadda ta matsa masa, sai ya faɗa mata cewar zai mayar da Hanifa wajen babarta.
Jamila ta ƙara da cewa a daren ranar na 5 ya sanar da ita zai mayar da Hanifa gida, a lokacin ta fara bacci, ya ce a ɗauko kayan makarantarta a saka mata.
Duk da ce masa da ta yi dare ya yi a lokacin 11 na dare, amma haka ya tafi kai ta a cewarsa.
“Lokacin da ya dawo na fara bacci, na kuma tambaye shi cewar ya mayar da yarinyar gida? Sai ya ce ‘e’.
“Bayan ƴan kwanaki sai na ga wata farar waya a hannunsa, sai na tambaye shi inda ya same ta sai ya ce min ta wani Hashimu Isyaku ce ya ba shi ya saka masa caji,” kamar yadda ta bayyana.