Mataimakin shugaban kasar Sin Han Zheng ya ce, Sin a shirye take ta yi aiki tare da sauran sassa wajen ingiza kyakkyawan yanayin cimma nasarar shawarar nan ta bunkasa duniya ko GDI.
Han Zheng ya bayyana hakan ne a jiya Talata yayin babban taron nazarin nasarar da aka cimma a fannin hadin gwiwar raya shawarar ta GDI, a taron da kasar Sin ta jagoranta a gefen taron kolin MDD na bana.
Kaza lika a cewarsa, bangaren Sin na fatan shiga a dama da shi wajen aiwatar da ajandar ci gaba mai dorewa ta MDD ta nan da shekarar 2030, tare da gina al’ummar duniya mai ci gaban bai daya.
Shawarar GDI, wadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar yayin taron kolin MDD karo 76 a shekarar 2021, na da nufin cimma daidaito tsakanin sassan kasa da kasa, a fannin ingiza ci gaba, da fadada bunkasuwar bai daya ta dukkanin kasashen duniya.
Bugu da kari, mataimakin shugaban kasar Sin Han Zheng ya ce kasarsa a shirye take ta yi hadin gwiwa da Guinea wajen goyon bayan juna a batutuwan da suka jibanci kare muhimman moriyarsu, tare da kare muradun sauran kasashe masu tasowa.
Han ya yi wannan alkawari ne a jiya Talata a lokacin da yake zantawa da shugaban rikon kwaryan Guinea Mamady Doumbouya, a gefen taron muhawara a babban zauren MDD dake gudana a birnin New York.
Kaza lika, a cewar mataimakin shugaban kasar Sin, kasarsa na jinjinawa Guinea bisa shiga rukunin masu goya bayan shawarar bunkasa duniya, kana Sin din ta shirya tafiya tare da Guinea wajen ingiza kawancen gargajiya dake tsakaninsu, da fadada cimma moriyar juna, da kara zurfafawa, da kafafa kyakkyawar dangantakar sassan 2. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Source: LEADERSHIPHAUSA