Osama Hamdan mai magana da yawun kungiyar Hamas a kasar Lebanon ya bayyana cewa duk wani shirin tsagaita budewa juna wuta a Gaza nan gaba sai ya hada da janyewar dukkan sojojin mamaya daga Gaza da kuma daukewa yankin dukkan takunkuman tattalin arzikin da aka dora masa.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Hamdan yana fadar haka a jiya Asabar a birnin Beirut na kasar Lebanon ya kuma kara da cewa kungiyar tana nazarin shawarwarin da aka gabatar na tsagaita budewa juna wata a yakin ta’addancin da HKI da kawayenta suke yi a Gaza, wanda ya kai ga kissan kiyashi ga mata yara tsoffi har da marasa lafiya.
Kafin hada dai gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa an fara tattauna batun tsaigaita budewa juna wuta a birnin Paris na kasar Faransa kuma tuni gwamnatin Yahudawa ta amince da wasu shawarwarin.
Ya zuwa yanzu dai sojojin yahudawa yan mamaya sun kashe falasdinawa fiye da dubu 28 a zirin Gaza daga ranar 7 ga watan Octon da ya gabata.

Source: IQNAHAUSA