Hamas; Za’a Fara Babbar Yaki Da Isra’ila Bayan Ramadan.
Daya daga cikin shuwagabannin kungiyar Hamas ya bayyana cewa za’a fara yaki babba bayan watan Ramadan, idan har jami’an tsaron gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta ci gaba da ta’asan da take aikawata a birnin Qudus a halin yanzu.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban kungiyar Hanas Yahyah Sinwar yana fadar haka a wani taro a birnin Gaza a jiya Asabar ya kuma bukaci dukkan dakarun kungiyar su yi shirin shiga yaki babba da yahudawan Isra’ila bayan watan Ramadan, idan har yahudawan sun ci gaba da keta hurumin masallacin al-Aksa .
A cikin makonnin da suka gabata , sau da dama jami’an tsaron HKI sun yi ta keta hurumin masallacin al-aqsa, musamman a lokutan bukukuwan yahudawa. Inda suka korar musulmi masu ibada a cikin masallacin.
READ MORE : Jami’an tsaro A Sudan Sun Tarwatsa Masu Zanga-zanar Cika Shekaru 3 Da Kisan Gilla Da Aka yi A Kasar.
Sinwar ya kara da cewa aikin mayakan kungiyar Hamas ne su kare hurumin wurare masu tsarki a kasar Falasdinu da aka mamaye, kuma masallacin alaksa na daga cikinsu.
READ MORE : Harin Bomb Da Aka kai a Birnin Kabul Yayi Sanadiyar Mutuwar Mutane 5 Tare Da Jikkata Wasu Da Dama.