Hamas Ta Yaba Da Jingine Maganar Baiwa Isra’ila Kujerar ‘Yar Kallo A (AU).
Kungiyar gwagwarmayar falasdinawa ta Hamas, ta bayyana jin dadinta game da matakin kungiyar tarayyar Afrika na jingine maganar baiwa Isra’ila kujerar ‘yan kallo a kungiyar.
Hamas, ta yi kira ga kungiyar ta AU, da ta yi aiki da dokokin da suka shafa yaunin da ya rataya a wuyanta na yaki da mamaya da nuna wariyar laujin fata da kuma kare hakkin falasdinawa.
Kasashe da dama ne dai na Afrika suke adawa da matakin da shugaban kwamitin kungiyar Musa Faki Mahamat ya gabatar na baiwa Isra’ila kujerar ‘yar kallo a kungiyar.
Aljeriya da Afrika ta Kudu, na daga cikin kasashen da suka amincewa da batun.
Majiyoyi da dama sun ce an dakatar da tattauna batun ne yayin taron koli na 35 don kada a haifar da rudani ko rashin jituwa tsakanin kasashe mambobin kungiyar ta AU.
Amma an ce an kafa kwamitin da zai tattauna batun da ya kunshi kasashe da dama.