Hamas; Kulla hulda Tsakanin Saudiyya da Isra’ila Cin Amanar Falasdinawa Ne.
A wata hira da gidan talabijin din press Tv na kasar Iran yayi da Mohamud Zihar kusa a kungiyar gwagarmaya ta Hamas game da batun yi yuwar kulla hulda tsakanin Saudiya da Isra’ila a ziyarar da shugaban Amurka Joe Biden zai kai yankin falasdinu da kasar Saudiyya, yace : kulla huldar cin amanar alummar falasdinu ne da ta ke fafutukar neman yanci daga mamayar yahudawan sahayuniya
Haka zalika ya kara da cewa kulla hulda tsakaninsu cin amanar jinin shaidai ne yan gwagwarmaya da alummar labarawa da ma kasashen musulmi sai dai kamar yadda Allah yayi Alkawari, nasara tana ga musulmi ne.
A bangare guda kuma ya soki wasu malami a kasar saudiya da suke nuna goyon bayan kulla hulda tsakanin Isra’aila da wasu kasashen larabawa ciki har da kasar Saudiya, yace duk wanda ya kulla hulda da Isra’ila to bashi da wuri a musulunci,
READ MORE : Shugaban Rasha Viladmir Putin Zai kawo ziyara Kasar Iran A Mako Mai Zuwa.
A yau laraba ce shugaban kasar Amurka Joe biden zai kai ziyara yankin falasdinu, kuma bayan ya kammala ganawa da mahukumtan Isra’ila kuma zai isa kasar Saudiya.
READ MORE : Joe Biden Na Kokarin Taimakawa Haramtacciyar Kasar Isra’ila A Ziarar Sa Zuwa Saudiyy.