A cikin wata sanarwa da suka fitar na ta’aziyyar shahadar Jihad Shakir al-Ghanam, Khalil Salah al-Bahtini, da Tariq Muhammad Ezzeddin, kwamandojin kungiyar Jihadin Islama ta Falasdinu, da wasu ‘yan kasar Falasdinu a Zirin Gaza, wadanda akasarinsu mata ne da kananan yara.
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) – ABNA – ya habarta cewa,
A cikin wata sanarwa da suka fitar na ta’aziyyar shahadar Jihad Shakir al-Ghanam, Khalil Salah al-Bahtini, da Tariq Muhammad Ezzeddin, kwamandojin kungiyar Jihadin Islama ta Falasdinu, da wasu ‘yan kasar Falasdinu a Zirin Gaza, wadanda akasarinsu mata ne da kananan yara. Kungiyar Hamas ta jaddada cewa gwamnatin sahyoniyawan za ta dandani Sakamakon laifukan da ta aikata.
A cikin wannan bayani, yayin da ake ishara da wuce gona da irin da gwamnatin sahyoniyawan ta yi a yankin Zirin Gaza, an jaddada cewa, cikakken alhakin wannan aika-aika na dabbanci da sakamakonsa yana kan gwamnatin sahyoniyawa da majalisar ministocinta fasikai masu tsattsauran ra’ayi.