Hamaas na kira ga Falasdinawa a Isra’ila da Gabar Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye da su tashi tsaye don nuna adawa da mamayar Isra’ila a cikin watan Ramadan mai alfarma da ke gabatowa.
Mai magana da yawun ƙungiyar Hamas, Osama Hamdan, da yake zantawa da manema labarai a birnin Beirut, ya ce Falasdinawa su sanya kowane lokaci na watan Azumin ya zamo wata arangama.
Kasashen Amurka da Qatar da Masar dai sun kwashe makonni suna kokarin ganin an tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas a Gaza da kuma shawo kan kungiyar masu fafutukar ganin an sako wasu adadi mai yawa na mutanen da ake garkuwa da su a harin na ranar 7 ga watan Oktoba.
An kama mutane da dama a sabon farmakin da Isra’ila ta kai a Yammacin Gabar Kogin Jordan da ta mamaye
Sojojin Isra’ila sun kama wasu Falasdinawa 55 a farmakin da sojojin suka kai a Yammacin Gaɓar Kogin Jordan da suka mamaye, a cewar kungiyoyin da ke kula da fursunoni.
A cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da hukumar kula da fursunonin Falasdinawa ta fitar ta ce, an kai aƙalla mutum 22 hannun Isra’ila a birnin Hebron, yayin da wasu kuma aka kama su a garuruwan Bethlehem da Ramallah, da ke Gabashin Kudus da kuma Qalqilya.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Kamen na nuni da ayyukan zagon ƙasa da lalata gidajen ‘yan kasar, baya ga mummunan duka da ake yi wa fursunonin da iyalansu, da kuma ƙwace kuɗaɗe.
Ministan Isra’ila ya yi kira da a taƙaita shigar Musulmai Masallacin Ƙudus a cikin watan Ramadan
Ministan Tsaron Isra’ila mai tsattsauran ra’ayi Itamar Ben Gvir, ya buƙaci ƴan sanda da su taƙaita shigar Musulmai Masallacin Ƙudus a cikin watan Ramadan mai alfarma, kamar yadda kafar yada labaran Isra’ila ta bayyana.
A yayin ganawar tasu, Ben Gvir ya shaida wa kwamishinan ‘yan sanda Kobi Shabtai da ya taƙaita yawan masu ibada a Ƙudus domin tabbatar da cewa ‘yan sanda sun shirya yin gaggawar mayar da martani ga duk wani hargitsi, kamar yadda jaridar Maariv ta Isra’ila ta ruwaito.
Jaridar ta kuma bayyana cewa, a ranar Litinin ne ake sa ran Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu zai tattauna batun hana shiga Masallacin Ƙudus tare da Ben Gvir Shabtai, da jami’an hukumar tsaro ta Shin Bet da kuma sojojin Isra’ila.
Mutane Da Dama Ne Suka Rasu A Cigaba Da Hare Haren Isra’ila
Adadin wadanda suka mutu a Gaza ya haura 30,534 yayin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare
Aƙalla Falasɗinawa 30,534 aka kashe a yayin yaƙin da Isra’ila ke yi a Gaza, kamar yadda Ma’aikatar Lafiya ta yankin da aka yi wa ƙawanya ta faɗa.
Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta ce aƙalla mutum 124 ne suka mutu yayin da wasu 210 suka jikkata a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, yayin da wasu 71,980 suka samu raunuka tun bayan yakin Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba bayan harin Hamas.
Ma’aikatar ta kuma bayyana cewa, Isra’ila ta aikata kisan kiyashi 13 a Gaza cikin sa’o’i 24 da suka gabata.
Mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris ta yi kira da a tsagaita wuta cikin gaggawa a Gaza.
DUBA NAN: Sabuwar Nasarar Sojojin Najeriya Kan ‘Yan Ta’adda
Mataimakiyar shugaban ƙasar Amurka Kamala Harris ta yi kira da a tsagaita wuta cikin gaggawa a Gaza tare da bayyana halin da ake ciki a Gaza a matsayin wani abu mai muni.