A daidai lokacin da kwanaki 13 ne suka rage a gudanar da tarukan zirarar arbaeen a halin yanzu a kasar Iraki, miliyoyin mutane daga ko’ina a cikin kasar suna ci gaba da yin tattaki zuwa Karbala.
Wanann yana zuwa ne a halin da a nasu bangaren mahukuntan kasar suke daukar dukkanin matakan da suka dace na kiwon lafiyar jama’a da kuma tsaro.
Muhimman hanyoyin da ake domin isa Karbala sun hada da Najaf – Haidariyya – Karbala, Hillah – Tuwairij – Karbala, Baghdad – Musayyib – Karbala, Ainu al-tamr – Karbala, Kufah – Tuwairij – Karbala.
A dukkanin wadannan hanyoyi mutane da suke a garuwa da kauyuka ne suke wa masu tattakin hidima da abinci da sauran abubuwan bukatar rayuwa.
A wani labarin nadaban hafin jaridar Yaum Sabi ya bayar da rahoton cewa, a jiya shugaban cibiyar kula da harkokin gidajen radiyo na kasashen musulmi Amru Laisi ya gana da babban malamin Azhar Sheikh Ahmad Tayyib a ofishinsa da ke birnin Alkahira.
A yayin wannan ganawa bangarorin biyu sun tattauna batutuwa da suka shafi ayyukan kafofin yada labarai na kasashen musulmi da kuma ayyukan da suke gudanarwa na wayar da kan al’umma.
Babban malamin na Azhar da kuma shugaban cibiyar kula da harkokin gidajen radiyo na kasashen musulmi sun cimma matsaya kan gudanar da taro na kasa da kasa na gidajen rediyon kasashen kasashen musulmi, musamamn na kur’ani.
Babbar manufar taron dai ita ce kara fayyace muhimman ayyuka da suka shafi sadarwa a kasashen musulmi, inda masana za su gabar da bayanai kan hakan
Baya ga haka kuma sun cimma matsaya kan bayar da horo na musamman dangane da ayyukan kafofin yada labarai an musulmi, wanda cibiyar Azhar za ta dauki nauyinsa.
An kafa cibiyar kula da harkokin gidajen radiyo na kasashen musulmi zaman taron karo na 6 na kungiyar kasashen musulmi ta OIC a shekara ta 1975, kuma wannan cibiya tana karkashin kungiyar kasashen musulmi ne.