Shida daga cikin Mahajjatan Nijeriya 95,000 masu aikin Ibadan hajji na bana sun rasu a kasar Saudiyya Arabiyya a kokarinsu na sauke farali.
Jagoran tawagar Likiticin da ke kula da alhazan Nijeriya, Dakta Usman Galadima, shi ne ya shaida hakan a Makkah jiya Asabar da daddare.
Da yake magana a lokacin ganawa da masu ruwa da tsaki kan shirye-shiryen hawa Arfa, Usman ya ce, biyu daga cikin mamatan Alhazan sun fito ne daga jihar Osun; daya Kaduna, wani Alhaji daga Filato.
Ya wasu alhazan sun mutu ne sakamakon bugun zuciya da sauran cutukan da bai bayyana ba.
Galadima, ya kara da cewa wasu alhazan 30 yanzu haka suna fama da jinyoyin da suka shafi matsalolin tabin hankali.
Ya tabbatar da cewa alhazan za su samu zarafin gudanar da aikin hajjinsu, “Yanayin da suke ciki yanzu da sauki sosai.”
Ya kara da cewa hatta mata masu juna biyu an samu a wannan hajji na bana a cewarsa, biyu masu juna biyu daga Sokoto, daya daga Adamawa, wata mahajjaciya mai juna biyu daga jihohin Kwara, Yobe, Filato da Katsina.
Galadima ya kara da cewa an samu masu zubar da ciki biyu, sannan wani Alhaji mai cutar Suga an yanke masa kafa.