Daruruwan mutane daga kasar Netherlands ne suka halarci zanga-zangar da aka yi a gaban kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa da ke birnin The Hague, inda suka bukaci a magance laifukan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a Gaza.
A cewar Anatoly, a wata zanga-zangar nuna goyon baya ga Falasdinu, daruruwan yara ‘yan kasar Holland da iyalansu sun yi tattaki zuwa ginin kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) da ke birnin Hague, inda suka bukaci a yi adalci da kuma gudanar da bincike kan laifukan da Isra’ila ta aikata a zirin Gaza.
Jama’a na addinai daban-daban da kuma kasashe daban-daban sun halarci wannan taron, wanda aka kira “Tattakin Yara”. Masu zanga-zangar sun yi ta rera taken “ICC, yi aikinku”, “‘Yancin Falasdinu” da “A daina bude wuta a yanzu”, masu zanga-zangar sun bayyana goyon bayansu ga al’ummar Palastinu da ake zalunta tare da dauke da alluna masu dauke da taken “Dakatar da kashe kananan yara”.
Ta hanyar daga tutocin Falasdinu, jama’ar da ke wurin sun ja hankali kan bukatar cika ayyukan kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa da kuma tinkarar rikicin na Gaza a halin yanzu.
Bilal Rayani shugaban gidauniyar Endulus kuma daya daga cikin wadanda suka shirya zanga-zangar ya ce abin da ke faruwa a Gaza ba yaki ne kawai ba, kisan kare dangi ne. Riyani ya kara da cewa: Dole ne kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta cika aikinta tare da gudanar da bincike kan kisan gillar da aka yi. Wadanda suke magana akai-akai game da Ukraine sun yi shiru game da Falasdinu.
Har ila yau, Larisa-Mae Hartkamp, daya daga cikin wadanda suka halarci tattakin, ta bayyana damuwarta game da samar da sassan yaki na F-35 da kasar Netherlands ta yi wa Isra’ila, inda ta jaddada cewa kamata ya yi a rika kallon Isra’ila a matsayin mai cin zarafi, ba mai kare kai ba.
A cikin sakon da ya aike wa Mark Rutte, Firayim Ministan Netherlands, ya ce: Rutte, ka daina goyon bayan kisan kare dangi! Hartkamp ya kara da cewa: “Mun yi tattaki zuwa kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa saboda muna son tsagaita bude wuta da adalci sannan kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ta yi aikinta.”
Hartkamp ya ci gaba da yin nuni da adadin ‘yan jaridan da suka mutu cikin kwanaki 80 da suka gabata ya kuma bayyana hakan a matsayin yunkurin Isra’ila na boye gaskiyar laifukan da ta aikata.
Source: IQNAHAUSA