Jagoran al’ummar yemen kuma babban shugaban kungiyar ansarullah mai iko da kasar yemen sheikh abdulmalik alhutsi ya bayyana cewa hadin kai da amurka ko haramtacciyar kasar isra’ila babbar barazana ce zaman lafiya da kwanciyar hankalin musulmin duniya baki daya.
Shugaban kuma jagoran al’ummar yemen ya bayyana hadin ka da isra’ila da wasu daga cikin kasashen larabawa sukeyi da isra’ila a matsayin babban kuskure wanda kuma zai cutar da al’ummar musulmi a duniya baki daya.
Babbar barazana ga musulmi itace hadin kai da manyan makiyan su wadanda babu sassauci a tsakanin su kamar amurka da isra’ila kamar yadda sheikh abdulmalik alhutsi ya bayyana yayin wani taro lokacin daya karbi bakunci shugabannin kabilun Aljubah da Alidiya dake yankin ma’arib ranar litinin a babban birnin kasar watau sana’a.
Yace makiya musulunci suna ta kokarin yakar musulmi ta cikin gida da waje inda ya bayyana saudiyya da hadaddiyar daular larabawa a matsayin na gaba gaba wajen yakar musulmi a fadin duniya baki daya dama kasar yaman.
Houthi yace babban aikin mu shine tabbatar dav hadin kai tsakanin musulmi gami da cigabantar da lamarin ‘yan uwantaka tsakanin al’ummar musulmi.
Ya bayyana cewa wadanda suka zabi su yaki al’ummar musulmi gami da yada rabuwar kai tsakanin musulmi sunci amanar kasashen su gami da mutanen su.
Kusan shekaru takwas kenan dai da aiwatar da juyin juya halin kasar yaman wanda al’ummar yaman din suka gabatar dashi domin samun canjin gwamnati daga ‘yan amshin shatan kasashen yammacin turai musamman amurka zuwa gwamnatin data damu da damuwar al’ummar yaman din.
Amma sai dai bayan gabatar da wannan juyin juya hali sai gamayyar kasashen ‘yan amshin sahatan amurka da kasashen yamma karkashin jagorancin saudiyya da hadaddiyar daular larabawa suka dirar ma yaman din wanda har zuwa yanzu ake ta fafata yaki babu ji babu gani, rayukan yara da tsofaffi gami da mata masu ciki da yawa ya salwanta sakamakon hare haren rashin imani na saudiyya.