Hadi matar, dan shekara 24 da ake zargi da kai wa Salman Rushdie hari ya ce ya yi mamaji jin marubucin bai mutu ba.
Matar, wanda a halin yanzu yana tsare a gidan yari a New York a bayyana hakan ne cikin hirar bidiyo da aka yi da shi.
Matashin ya bayyana cewa baya kaunar Rushdie domin yana sukar addinin musulunci da abin da musulmai suka yi imani da shi.
Mutumin da ake zargi da caka wa Salman Rushdie wuka a wurin wani taro a New York Amurka ya ce ya yi “mamakin’ gano cwa fitaccen marabucin yana da rai bayan harin, Metro UK ta rahoto.
Hadi Matar, mai shekara 24, ya ce Salman, mai shekara 75, mutum ne ‘wanda ke sukar musulunci’ amma bai tabbatar da cewa ya kai masa harin bane biyo bayan fatawa da Jamhuriyar Musulunci Iran ta yi a shekarun 1980s.
Hadi ya ce bai aikata wani laifi ba ta bakin lauyansa bayan an gurfanar da shi a kotu kuma a yanzu yana tsare a gidan yari na Chautauqua a Jihar New York, The Cable ta rahoto.
A hirar da New York Post ta yi da shi a bidiyo daga gidan yarin, ya ce: “Da na ji cewa bai mutu ba, na yi mamaki”.
Matar ya ce ya yanke shawarar zuwa taron ne a Chautauqua bayan ganin sanarwar a Twitter cewa Salman zai hallarci taron.
“Bana son mutumin. Bana tunanin mutumin kirki ne. Bana son sa sosai.”
“Yana sukar musulunci, yana sukar abin da suka yi imani da shi,” in ji shi. Salman ya wallafa littafinsa mai suna ‘Satanic Verses a 1988’, wacce hakan yasa Shugaban Iran, Ayatollah Ruhollah Khomeini ya yi fatawa ne halasta jininsa a 1988.
Amma, matar, ya ce shafuka kadan ya karanta a littafin kuma bai bayyana ko fatawar ce tasa ya kai harin ba.
“Ina girmama Ayatollah. Ina masa kallon babban mutum. Wannan kawai shine abin da zan ce kan hakan,” in ji shi.
Salman Rushdie da Ya Yi Batanci Ga Annabi Na Can Rai Hannu Rabbana a Asibitin New York Tunda farko, Salman Rushdie, marubuci dan Indiya da rubutunsa ya kai ga barazanar kisa daga gwamnatin Iran a shekarun 1980, an caka masa wuka a lokacin da yake shirin gabatar da lacca a kudu maso yammacin jihar New York.
‘Yan sanda sun tabbatar da cewa an caka wa Rushdie wuka a sau daya a wuya kana sau daya a cikinsa a ranar Juma’a bayan da wani mahari ya yi zafin naman farmakarsa a kan dandamali.
Source:legirhausang