Habasha; Firai Ministan Kasar Ya Ce A Shirye Yake Ya Fara Tattaunawan Da ‘Yan Tawayen Tigray.
Firai ministan kasar Habasha Abiy Ahmed ya bayyana a fili kan cewa gwamnatinsa na duba yiyuwan shiga tattaunawa da yan awaren Tigray a karon farko bayan fafatawa na watannin 19.
Shafin yanar gizo na labarai ‘AfricaNews’ ya nakalto Abiy yana cewa gwamnatinsa ta kafa kwamiti na musamman don duba yiyuwan shiga tattaunawa da yan awaren na Tigray, babu ba gaskiya ne , gwamnatin tana tattaunawa da su a asirce kamar yadda wasu ke fada ba.
Firai ministan ya kara da cewa tattaunawa da yan awaren ba mai sauki bane, don haka ne ma ya kafa kwamiti don yin wannan aikin. Kuma mataimakin firai ministan kasar Demeke Mekonen shugaban kwamitin wanda har’ila yau shine ministan harkokin wajen kasar.
Ya ce shi ne zai tattara bayanai sannan ya gabatar da rahoton kan yadda tattaunawar zata kasance idan zata yu, da kuma matsalolin da suke iya kawo cikas a tattaunawar. Yakin na watanni 19 dai ya tialstawa mutane kimani miliyon 2 kauracewa gidajensu sannan wasu miliyon 9 suna fama da karancin abinci a yankin.
Ya zuwa yanzu dai gwamnatin Abiy ta fara shirin bude hanya don isar da kayakin agaji zuwa yankin.