Wasu Gwamnonin Najeriya da suka fito daga Yankin Arewa maso Yamma na shirin gudanar da taro da takwarorin su na Jamhuriyar Nijar da suka hada iyaka domin tattauna batutuwan da suka shafi tsaro a tsakanin su.
Tambuwal yace zasu gudanar da taron ne da gwamnonin jihohin Dosso da Tahwa da kuma Maradi, kuma cikin gwamnonin Najeriya da zasu halarci taron harda takwarorin sa na jihohin Zamfara da Katsina.
Gwamnan ya bayyana cewar abin takaici ne yadda matsalar rashin tsaro ta dabaibaye yankin na su, yayin da ya kara da cewa suna iya bakin kokarin su a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari domin dawo da zaman lafiya a jihohin dake kan iyakokin.
Tambuwal ya mika sakon godiya daga shugaba Buhari zuwa shugaba Bazoum Muhammad akan karimcin da suka musu na kula da dubban ‘Yan gudun hijirar da suka tsugunar daga Najeriya.
Najeriya da Jamhuriyar Nijar na ci gaba da fuskantar hare haren ‘Yan ta’adda daga sassa daban daban na kasashen su wadanda ke kai munanan hare haren dake sanadiyar rasa dimbin rayuka.
A wani labarin na daban rahotanni daga Najeriya na cewa ‘yan bindiga sun hallaka jami’an tsaron kasar 12 a wani farmaki kan sansanin Sojin kasar da ke jihar Zamfara a yankin arewa maso yammacin kasar.
Har zuwa yanzu dai babu cikakken bayani wadanda suka kaddamar da farmakin, wanda bayanai ke cewa ya faru a Mutumji cikin ranakun karshen mako.
Har yanzu Sojin Najeriyar na ci gaba da fatattakar maboyar ‘yan bindigar jihar ta Zamfara matakin da ke zuwa bayan katse layukan sadarwa don magance matsalar da ta addabi jihar da makwabtanta.