Gwamnatin Zimbabwe ta gayyaci jakadan Amurka a kan saƙonni a shafukan intanet
Gwamnatin Zimbabwe ta gayyaci mukaddashin jakadan Amurka a kasar a kan wasu sakonni da ya rubuta a shafun sada zumunta da muhawara, wadanda gwamnatin ta ce na katsalandan ne a harkokin cikin gidanta.
A makon da ya gabata ne ofishin jakadancin Amurkar ya yi kira ga ‘yan Zimbabbwe da su je su yi rijista domin su yi zabe kuma su tabbatar kuri’arsu ta yi tasiri.
A wata sanarwa da ta fito daga Rofina Chikava, da ke rikon mukamin babbar sakatariya a ma’aikatar harkokin wajen kasar jiya Talata, ta tabbatar da gayyata da kuma ganawar.
Ta gaya wa babbar jami’ar da ke kula da harkokin yau da kullum a ofishin jakadancin Amurka cewa ba su yarda da irin wannan rubutu ba domin ya kauce wa tsarin huldar diflomasiyya.
Wata mai magana da yawun ofishin jakadancin Amurka a Zimbabwe din ta ce su a wajensu babu wata matsala dangane da wannan sako, amma kuma ta tabbatar da gayyatar da kuma ganawar.
Ana kara samun yanayi na zaman dar-dar ya yi da kasar ke shirin gudanar da babban zabenta.
Read More :
Sojojin Sudan sun janye daga yarjejeniyar dakatar da buɗe wuta in ji wasu kafofi.