A jiya Asabar gwamnatin mulkin sojin Myanmar ta sanar da yin afuwa ga fursunoni sama da 800, a yayin da ta gudanar da faretin nuna kwanji a babban birnin kasar don bikin tunawa da ranar samun yancin kai shekaru 75 da suka wuce.
Shugaban gwamnatin soji Min Aung Hlaing ya bada wannan umurni na sakin fursunoni 814, abin da aka saba yi a rana irin wannan.
Ana bikin an shekara shekara ne don tunawa da ranar da jagoran gwagwarmayar neman yancin kai, Aung San da kabilu da dama suka shiga yarjejeniyar yanto Burma daga mulkin mallakar Birtaniya.
A wani labarin na daban Wata Kotu a kasar Myanmar ta daure tsohuwar jagorar gwamnatin kasar Aung San Suu Kyi shekaru 4 a gidan yari, saboda samun ta da laifin tinzira jama’a su yiwa sojoji bore da kuma kin mutunta dokar yaki da annobar korona.
Mai magana da yawun gwamnatin kasar Zaw Min Tun ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar, kotun ta daure Suu Kyi shekaru 2 a gidan yari saboda laifin tinzira yiwa sojoji bore, yayin da aka kara mata wasu shekaru 2 saboda kin mutunta dokar hadura ta kasa wadda ta shafi annobar korona.
Shima tsohon shugaban kasar Win Myint ya gamu da daurin shekaru 4 sakamakon irin wadannan tuhume tuhumen guda biyu, yayin da jami’in yace ba za’a yi gaggawar kai su gidan yari ba saboda akwai sauran tuhumar da ake musu.
Ita dai kotun ta haramtawa ‘Yan Jaridu sauraron shari’ar, yayin da ta kuma haramtawa lauyoyin wadanda ake tuhuma damar yiwa jama’a bayanin abinda ya faru a cikin ta.
Tuni kungiyar Amnesty International tayi Allah wadai da hukuncin, yayin da ta zargi gwamnatin sojin da kokarin dakushe ‘yancin jama’ar kasar.
Sanarwar da kungiyar ta gabatar yace wannan hukuncin mai tsanani da kotun Myamar ta gabatar akan Suu Kyi wata alama ce ta kawar da masu adawa da ita da kuma dakushe ‘yancin jama’a.