Gwamnatin Mali ta ce za ta kaddamar da shirin jin ra’ayin jama’a a wannan watan, kafin sanya lokacin gudanar da zaben shugaban kasa.
Shugaban mulkin sojin kasar Assimi Goita yayi alkawarin gudanar da zabe a watan Fabarairu, amma kuma gwamnatin sa na jan kafa a kai.
Kasar na yankin sahel da yaki ya daidaita na fuskantar matsin lamba daga kasashen duniya a game da mayar da mulki ga farar hula, bayan da sojoji suka kifar da zababbiyar gwamnatin kasar a watan Agusta 2020, ta kuma kori wata gwamnatin a watan Mayu.
A wani labarin na dabna gwamnatin kenya ta ki amincewa da hurumin Kotun Majalisar Dinkin Duniya (ICJ), dake shirin yanke hukunci a mako mai zuwa kan takaddamar iyakokin teku da ta dade tana yi da Somaliya
Tun a watan Maris Kenya ta sanar da shirin kauracewa zaman kotun ICJ a shari’ar da tuni kotun da ke Hague ta ki amincewa da bukatar dage ta, inda ake saran zartar da hukunci a ranar Talata mai zuwa.