Gwamnatin Habasha ta ce dakarunta sun yi nasarar kwato garuruwa da dama daga hannun ‘yan tawayen TPLF a yankin Tigray, da suka hada da Kobo da Woldiya a arewacin kasar, bayan kazamin fadan da aka gwabza a yakin da kawo yanzu aka shafe watanni 13 ana yi, wanda ya yi sanadin mutuwar dubban mutane.
A baya bayan nan, hukumar kare hakkin dan Adam ta Majlisar Dinkin Duniya ta amince da tura tawagar masu bincike zuwa arewacin Habasha, domin tantance zarge-zargen aikata laifukan yaki a tsakanin dakarun kasar da mayakan ‘yan tawaye, musamman ma kan cin zarafi da ake zargin yi wa mata.
Tun daga karshen watan Oktoba, bangaren gwamnati da na ‘yan tawaye ke ikirarin samun nasarar mamaye karin yankuna a arewacin Habasha.
A ranar Lahadin da ta gabata ‘yan tawayen TPLF suka sake kwace garin Lalibela da ke kunshe da wurin tarihi na hukumar UNESCO ta Majalisar Dinkin Duniya, kwanaki 11 bayan da dakarun gwamnatin Habasha suka yi ikirarin kwace garin daga hannun ‘yan tawayen.
A watan Nuwamban shekarar 2020 yaki ya barke a Tigray, bayan da Firaminista Abiy Ahmed ya aika da sojoji zuwa yankin da ke arewacin kasar, domin kawar da kungiyar ta TPLF, da ya zarga da kai hare-hare kan sansanonin sojoji.