Gwamnatin Habasha Na Ganawar Sirri Da Mayakan Tigray.
Gwamnatin Habasha da kuma mayakan dake fafatukar a ware na yankin Tigray, sun koma bakin wata tattaunawa dake gudana cikin sirri, a Djibouti a shiag tsakanin Amurka.
Ganawar za ta fi maida hankali ne kan batun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma kawo karshen killacewa ko matakan da gwamnatin Aby Ahmed ta dauka kan yankin na Tigray.
Baya ga hakan akwai kasantuwar dakarun Eritrea dake yaki tare da na Addis Ababa, sai kuma batun yankin nan da ake takkama kansa na Wolkait dake yammacin Tigray.
Wakilin Amurka a yankin kahon Afrika ne Mike Hammer, ya shirya ganawar.
Rahotanin sun ce za’a kwashe kwanaki da dama ana tattaunawar.
Rikici tsakanin bangarorin ya sake barkewa ne a karshen watan Agusta bayan shafe watanni biyar na tsagaita wuta.
READ MORE : Najeriya Na Yunkurin Sasanta Ivory Coast Da Mali.
Wannan ita ce ganawa irinta ta farko tun bayan sake barkewar fada tsakanin bangarorin biyu a arewacin kasar.
READ MORE : Iran Ta Caccaki Sabbin Takunkuman Amurka.
READ MORE : Aikin karamin ofishin jakadancin Iran a Karbala zai kasance awanni 24 a ran
READ MORE : Elizabeth II: Shugaba A Afirka Ya Ayyana Zaman Makoki Na Kwana 3.