Jaridar The Point ta bayar da rahoton cewa, a yau shugaban kasar Gambia Adama Barrow ya sanar da ranar 10 ga watan Muharram wato ranar Ashura wanda zai kama a ranar Alhamis mai zuwa a matsayin ranar hutu a hukumance a fadin kasar, kamar yadda gwamnatin kasar ta tabbatar da hakan.
Shugaban kasar ta Gambia ya ce, baya ga kasancewar ranar Alhamis tana ce ta Ashura, haka nan kuma ta yi daidai da ranar 16 ga watan Agusta, ranar da mabiya addinin kirista suke girmamawa,a matsayin cewa a ranar ne ruhin Sayyida Maryam (AS) ya tafi sama.
Shugaba Adama Barrow ya ce har kullum musulmi da kirista suna rayuwa cikin zaman lafiya da kwanciya hankali da fahimtar juna da kuma girmama a kasar Gambia, wanda a cewarsa wannan babban abin alfahari ga daukacin al’ummar kasar dama gwamnatin kasar.
Kimanin kashi 95% na mutanen kasar Gambia dai musulmi ne, galibinsu kuma mabiya darikar Tijjaniya ne.
Masana daga bangarori da dama sun yabawa wannan namijin kokari da gwamnatin ta gambia tayi kuma an bukaci sauran kasashen afirka suyi koyi da wanna kyakykyawan salon shuganaci na Adama Barrow.
Daga jamhuriyar musulunci ta Iran kuma Mohsen Isma’ili malamin jami’ar Tehran ya bayyana cewa, abin da ya faru da zuriyar manzon Allah (SAW) na tozarci da kisan kiyashin da masu kiran kansu musulmi suka yi musu shi ne abu mafi muni da ya faru shekaru bayan wafatin manzon rahma.
Ya bayyana hakan ne a bayanin da yake gabatarwa wanda ake watsawa ta hanyar yanar gizo wanda masu bibiyar bayanan a cikin harshen farisanci sukan tarjama su zuwa wasu harsuna domin amfanin al’ummar musulmi.
Tarihi dai ya tabbatar da cewa makiya iyalan gidan manzon (S) sunyi iyakan kokarin su domin boye lamarin hadisar ashura amma cikin nufin Allah ta’ala basu iya cimma muradan su ba, sai da labarin ashura ya tambatsa a duniya.