Gwamnatin Buhari Ta Bada Kontiragin Kula Da Tsaron Layin Dogo Da Tashoshinsa.
Gwamnatin Najeriya ta bada kontragin tsaron layin dogo tsakanin Abuja da Kaduna ga wasu kamfanonin tsaro masu zaman kansu.
Jaridar premium times ta Najeriya ta nakalto ministan babban birnin Tarayya Mohammaed Bello yana fadar haka a ranar laraba bayan taron majalisar ministocin kasar wanda shugaba Buhari ya jagoranta.
Bello ya kara da cewa saboda harin da aka kaiwa wani jirgin kasa a cikin watan Maris da ya gabata gwamnatin shugaba Buhari ta amince a bada kwangila na naira miliyon N718.19 ga kamfanonin tsaro guda biyu wadanda zasu kula da tsaron layukan dogo da tashoshinsa daga birnin Abuja zuwa Kaduna.
A cikin watan Maris da ya gabata ne ‘yan ta’adda suka dana bom kan layin dogo tsakanin biranen biyu, wanda ya yi sanadiyyar faduwar wasu taragogin jirgin kasa dauki da fasinjoji kimani 1000.
Sannan banwa wadanda suka rasa rayukansu da kuma ji rauni, har yanzun akwai fasinjojin jirgin da suke tsare a hannun ‘yan ta’addan da ransu.
Kamfanonin da aka bawa wannan aikin dai sun hada da Al-Ahli Security Guards Limited and Messers Seaguard Security and Protective Company Limited. Kuma aikinsu ya hada da kare layukan dogo tashoshinsu, da cibiyoin sadarwa na kamfanin jiragen kasa na kasar.