Gwamnati ta fara sassauta dokokin kulle a kasar Saudiya yayinda Korona ta fara sauki. Hakazalika.
Saudiyya ta sanar da cewa za’a gudanar da hakkin Hajji bana An amince a sha shisha a wuraren shan gahawa a Saudiyya daga ranar Litinin yayin da ake sassauta dokar kullen korona a ƙasar, rahoton Saudi Gazzete.
Bayan shekara guda, Saudiyya ta fara sassauta dokokin kulle sakamakon annobar cutar Korona. Cikin sharrudan da ma’aikatar kula da birane da karkara ta gindaya domin amincewa mutum ya shiga shagon Shisha shine ya kasance ya yi rigakafin Korona.
Hakazalika wajibi ne dukkan ma’aikatan shagunan su rika yin gwajin korona mako-mako.
Hakazalika, wajibi ne bada tazara kuma a sarari za’a sayar. Bayan haka, sau daya za’a yi amfani da tiyo guda wajen shan Shisha kuma kada mutum sama da biyar su sha a lokaci guda.
Ma’aikatar ta bayyana sharruda ne a manhajarta na Tawakkalna, bangare guda, Yariman Saudiyya mai jiran gado Muhammad bin Salman bin Abdulaziz da mataimakin Firaminista da kuma ministan tsaro sun tattauna da shugaban sojin Chadi Mahamat Idriss Deby ta wayar tarho a ranar Lahadi.
Alarabiya News ta ruwaito cewa, Yarima bin Salman ya yi wa Janar Mahamat Deby ta’aziyyar rasuwar mahaifinsa Idriss Deby wanda ya rasu a ranar Litinin sakamakon samun wasu raunuka a fagen daga.
Hakan na zuwa a lokacin lamurra suka tsamama a kasar palestine inda ake ganin gwamnati ta saudiyya da hannu dumu dumu a goyon bayan zaluncin da yahudawan haramtacciyar kasar isra’ila suke aiwatarwa a kan raunanan falasdinawa wadanda basu ji ba basu gani ba.
Gwamanti mai mulkin saudiyya dai tana cikin abokan yahudawan haramtacciyar isra’ila na kusa kusa wanda hakan yake nuni da goyon bayan masaurautar saudiyya din ga ta’addancin da gwamnati mai iko haramtacciyar kasar isra’ila take aiwatarwa a kan raunana falasdinawa.
Isra’ila dai ta dage wajen kashe fararen hula falasdinawa amma an kasa samun kwakwkwaran motsi daga bangaren gwamnatocin kasashen labarawa.