Simon Lalong ya tabbatar da cewa ya ji sunan sa a cikin wadanda ake tunanin dauka a jam’iyyar APC Gwamnan jihar Filaton ya nuna zai fi kyau Bola Tinubu ya tafi da Kirista, a maimakon ya dauki Musulmi.
Shugaban Gwamnonin na Arewa yace baya ga lashe zabe, ya kamata APC ta duba yadda za a zauna lafiya.
Nan da gobe ake jiran duk wata jam’iyyar siyasa ta tsaida wanda zai yi mata takarar mataimakin shugaban kasa a zaben da za ayi a 2023.
Daily Trust ta tattauna na musamman da Gwamna Simon Lalong a kan maganar wanda ya kamata ya zama abokin takarar Bola Ahmed Tinubu.
Gwamnan na jihar Filato ya nuna cewa ya fi yarda da siyasar da ake tafiya da kowane bangare. Irin haka gwamnatinsa ke gudanar da mulki a Filato.
Shugaban gwamnonin Arewacin Najeriya ya na ganin zai fi kyau Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya dauki Kirista. Lalong yana neman takara?
Simon Lalong ya tabbatarwa Trust TV ya ji yana cikin wadanda za a iya ba takarar mataimakin shugaban Najeriya a jam’iyyar APC a zabe mai zuwa.
Gwamnan na Filato yace ba yana harin takarar ba ne saboda addininsa, sai don ya cancanta, domin akwai bukatar a tafi da kowane bangare.
Gwamna Simon Bako Lalong Hoto: www.sunnewsonline.com Asali: UGC Har ila yau, Mai girma gwamnan ya yi bayanin rawar da gwamnonin Arewa suka taka wajen ganin an shawo kan duk wata matsala a zaben ‘dan takara.
“Lokacin da mu ka dauke su (mutum 5 masu neman yin takarar shugaban kasa), ba mu yi maganar addininsu ba, a siyasa akwai abin da aka saba da shi.”
Tinubu ya nuna wanda yake so ya zama Mataimakinsa a zaben 2023 “Idan mutane sun yarda da irin wannan al’ada, da zarar kayi yunkurin hana su abin da aka saba da shi, hakan na nufin ka na cire su daga lissafi kenan.”
Simon Bako Lalong Musulmi da Musulmi?
A hirar, Lalong ya yi maganar a hada takarar Musulmi da Musulmi a APC, ya ce idan ana neman zaman lafiya da kwanciyar hankali, bai dace ayi haka ba.
“Mu na maganar kasa ta zauna lafiya. Yanzu haka mu na cikin rikici. Shawo kan rikici ba cin zabe ba ne kurum, har da yadda za a shugabanci kasar.”
“Idan aka fara tunanin wannan, dole ayi la’akari da kowa, a nuna masu za a dama tare da su.”
Simon Bako Lalong Tinubu zai dauki Kiristan Arewa?
Rahotanni na nuna a yau za a san abokin takarar Bola Tinubu a Jam’iyyar APC, kuma alamu na kara nuna cewa takarar Musulmi da Musulmi na neman tabbata.
Atiku na daf da daukar Gwamna mai-ci, Tinubu zai tafi da tsohon Gwamna Bola Tinubu ya nuna sha’awar tafiya da yankin Arewa maso gabas, watakila zai dauki Sanata mai wakiltar Borno