Gwamantin Mulkin Soji Ta kasar Sudan Ta Janye Dokar Ta Ba ci Da Ta Sanya A Kasar.
Shugaban mulkin soji na kasar Sudan ya sanar da cire dokar ta baci da aka sanya a kasa biyo bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan oktoban shekarar da ta gabata, bayan da kasar ta fuskanci gagarumar zanga-zangar adawa da mulkin soji a kasar
Wannan matakin ya zo ne bayan da Janaral Abdul-fatah burhan shugaban majsaliar koli ta mulki a kasar ya sanar da hakan yan sao’I bayan da cibiyar tsaro ta kasar ta cimma matsaya kan batun.
A baya bayan nan manzon musamman na majalisar dinkin duniya a kasar Sudan ya nuna takaicinsa game da kashe wasu masu zanga-zangar nuna adawa da mulkin soja a kasar, a birnin khartum a ranar Asabar da ta gabata, kuma an kashe mutanen guda biyu ne a lokacin zanza-zanga a yankin Kalakla dake makwabtaka da birnin khartum.
Zanga-zangar ta ranar Asabar wani bangare ne ta nuna adawa da mulkin soji a kasar, inda daruruwan mutane suka yi jerin gwano a babban birnin kasar don neman a a koma aiki da kundin tsarin mulkin kasar , daruruwan mutane ne aka kashe daga lokacin fara zanga-zanar a shekarar bara zuwa yanzu kamar yadda majiyar lafiya ta kasa ta sanar.