Kamar yadda Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na – ABNA – ya nakalto maku daga kamfanin dilanci labarai na IRNA cewa Mayakan gwagwarmaya na bataliyoyin Saraya Al-Quds sun far wa sojojin yahudawan sahyuniya inda suka kashe wasu daga cikinsu tare da jikkata wasu daga cikinsu.
Kamfanin dillancin labaran Irna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Al-Mayadeen cewa a yau talata bataliyoyin Saraya Al-Quds sun sanar da cewa sun kai farmaki kan wasu sojojin yahudawan sahyoniya da suke boye a wani gida a birnin Khanyounis.
Bataliyar ta sanar da cewa an harba wa sojojin yahudawan sahyoniya makaman roka na “TBJ”, kuma a sakamakon wannan harin an kashe wasu daga cikinsu, wasu kuma sun jikkata.
Dangane da haka ne kuma kafafen yada labaran gwamnatin sahyoniyawan suka rawaito cewa kungiyar Hamas a jiya ta gargade mu cewa har yanzu yakin bai kare ba tare inda ta kai hare-haren wuce gona da iri daga yankin Rafah.
A safiyar yau talata ne sojojin gwamnatin sahyoniyawan suka sanar da mutuwar jami’anta da sojojinta guda hudu tare da raunata wasu 6 a fadan da aka gwabza a kudancin zirin Gaza a daren jiya wanda adadin sojojin da aka kashe tun farkon harin 7 watan Oktoba ya kai mutane 514.
Tun da aka fara yakin guguwar Al-Aqsa a kowace rana sojojin yahudawan sahyoniya suna bayyana sunayen sojojin da suka rasa rayukansu, An gudanar da wannan mataki ne saboda yawan hasarar da sojojin yahudawan sahyoniya suke yi a yakin Gaza da kuma fargabar karin martani a matakin cikin gida a yankunan da suke mamaye da su.
Ana fitar da kididdiga da sunayen sojojin gwamnatin yahudawan sahyoniya da aka kashe a yakin Gaza bisa umarnin wannan gwamnati da kuma bayan ba da izini na musamman, kuma sunayen da aka bayyana ba su ne ma’auni na hakikanin adadin wadanda aka kashe ba.
Kafafen yada labaran yahudawan sahyoniya sun rawaito cewa adadin wadanda suka samu raunuka da sojojin Isra’ila suka sanar ya sha banban da adadin da asibitocin wannan gwamnati ke bayarwa.
Gwamnatin yahudawan sahyoniya ta shafe kwanaki 94 tana kai hare-haren bama-bamai a wuraren zama da cibiyoyin kiwon lafiya da al’adu a zirin Gaza a matsayin ramuwar gayya kan hare-haren da guguwar Al-Aqsa ta kai da kuma neman rama gazawarta da tayi tare da kuma dakatar da ayyukan gwagwarmaya amma hakan bai cimmawa ruwa ba.
Source: ABNAHAUSA