Gwagwarmaya ce Hanyar Daya Tilo Ta Dawo Da Hakkokin Falasdinawa.
Ministan ala’adu da koyarwa musulunci na kasar iran Mohammad Mahdi Esmaili da ministan al’adu na kasar labanon Mohammad Wissam murtadha acikin wani jawabin bayan taro na hadin guiwa da suka fitar sun jaddada game da muhimmancin rungumar hanyar gwagwarmaya a matsayi mafita ta dawo da dukkan hakokin falasdinawa da Isr’ila ta danne musu. Da kuma yanto masallacin Kudus mai tsari
Munanan Ayyukan da gwamnatin yahudawan sahyuniya take aikatwa a yankunan falasdinawa da ta mamaye ya sabama yancin fadin albarkacin baki da mutuncin dan Adam kuma ya nuna bakar aniyarta a idon duniya.
Hr ila yau sun kara da cewa gwamnatin sahyuniya ta mamaye yankunan falasdinwa tana ci gaba da yin kisan gilla da rusa ababen tarihinta na gado .
Ya kara da cewa ko a ranar laraba da ta gabata sun kai hari a sansanin yan gudun hijira na Jenin tare da kashe yar rahoton gidan talabijin din Aljazeera Shirin Abu Akle.
Ita dai Yar jaridar ta fara aiki da gidan talabijin din Aljazeera ne tun a sheraka ta 1997 kuma ta yi shahadane ne adaidai lokacin da take hada rahoto kan samamen da sojojin Isra’ila suka kai a sansanin falasdinawa na jenin.