Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince ba tare da hamayya ya bai wa Sakatare Janar na majalisar Antonio Guterres damar yin wa’adi na biyu domin ci gaba da tunkarar matsalolin da suka addabi duniya musamman rikice-rikicen da ake fama da su.
Guterres wanda tsohon Firaministan Portugal ne ya karbi aikin jagorancin Majalisar ne a shekarar 2017 daga hannun Ban Ki Moon, tsohon Jakadan kasar Koriya ta Kudu.
Akalla ‘yan takara 10 suka nemi mukamin, amma bukatarsu ba ta samu karbuwa ba saboda babu wata kasa daga cikin kasashe 193 na Majalisar da suka goya musu baya.
Yayin wani zama na musamman da aka yi a asirce, daukacin kasashe 15 da ke kwamitin sulhu sun amince da bukatar sake bai wa Guterres damar rike mukaminsa domin yin wa’adi na biyu kamar yadda shugaban kwamitin Sven Jurgenson, Jakadan Estonia ya bayyana.
Ana sa ran gabatar da sunan Guterres ga babban zauren Majalisar Dinkin Duniya domin amincewa da nadin nan bada dadewa ba.
A wani labarin na daban kasar Sudan ta bukaci taimakon Jamhuriyar Nijar wajen warware rikicin Kogin Nilu dake gudana tsakanin kasar da Masar da kuma Habasha.
Ministar harkokin wajen kasar Mariam Al Mansoura Al Sadiq Al Mahdi ta bayyana bukatar lokacin da ta ziyarci shugaban Nijar Bazoum Mohammed a fadar sa dake birnin Yammai.
Fadar Bazoum tace Ministar tare da shugaban kasar sun tattauna batutuwa da dama da suka kunshi dangantaka tsakanin kasashen biyu da kuma harkokin da suka shafi kasashen Afirka da duniya baki daya.
Al Mansoura ta bukaci shugaba Bazoum da yayi amfani da matsayin Jamhuriyar Nijar da kujerar da take da shi a Kwamitin Sulhu wajen sasanta takaddamar da ake cigaba da yi dangane da gina madatsar ruwan Habasha akan Kogin Nilu wanda zai hana Masar da Sudan ruwa.
Ministar ta kuma bukaci shugaban da ya kafa ofishin Jakadan Nijar a Khartoum domin bunkasa danganta tsakanin kasashen biyu, yayin da Sudan ke da nata ofishin a birnin Yammai.
Sanarwar tace shugaba Bazoum Mohammed ya saurari bakuwar ta shi kuma ya bayyana shirin amfani da matsayin Nijar wajen tabbatar da zaman lafiya a Gabashin Afirka.