Guterres Ya Damu Game Da Ruruwar Wutar Rikici Tsakanin Falasdinu Da Isra’ila.
Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya nuna matukar damuwa game da halin da ake ciki na ruruwar wutar rikici tsakanin Faladina da Isra’ila.
Kakakinsa Mr. Stephane Dujarric, ya ce Guterres na bibiyar yanayin da ake ciki a yankunan Falasdinu da aka mamaye da na Isra’ila.
Ya kuma kadu da jin rasuwar fararen hula da dama, ciki har da mata da kananan yara.
Ya ce ya zama wajibi sojojin Isra’ila su kaucewa amfani da karfin tuwo, ko makamai masu hadari, har sai hakan ya zama ba makawa domin kubutar da rayuwar jama’a.
A halin da ake ciki dai ana zaman dar dar a yankunan Falasdinawa da Isra’ilar ta mamaye musamman a garin Jenin da ke arewacin gabar yammacin kogin Jordan a cikin ‘yan kwanakin nan.
READ MORE : Tarayyar Turai EU Ta Sanar Da Dakatar Horar Da Sojojin Kasar Mali.
Hakan dai ya zo ne a daidai lokacin da firaministan Isra’ila Naftali Bennett ya baiwa dukkan jami’an soji da na tsaro cikakken ‘yancin gudanar da ayyukansu a yankunan, furucin da ma’aikatar harkokin wajen Falasdinu ta dauka a matsayin umarni na kashe Falasdinawa.
READ MORE : Sudan; Ana Gudanar Da Gagarumar Zanga-Zangar Neman Kafa Gwamnatin Farar Hula Zalla.