Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi tur da sabbin hare-haren da Rasha ta kaddamar a yankin gabashin Ukraine, yayin da ya yi kira da a cimma yarjejeniyar kwanaki hudu domin bai wa fararen hula damar ficewa saboda bikin Easter.
Guterres ya koka kan cewa, a maimakon a gudanar da bikin sabuwar rayuwa a wannan lokaci, amma hare-haren na Rasha a gabashin Ukraine sun ci karo da bikin Easter.
Babban Magatakardar na Majalisar Dinkin Duniya ya shaida wa manema labarai cewa, wannan yakin na Ukraine ya dada rincabewa tare da karin zubar da jini da lalata wurare sakamakon kaimin da aka kara na farmakin soji.
Guterres ya bukaci a tsagaita musayar wuta saboda alfarmar bikin Easter daga ranar Alhamis zuwa Lahadi, 24 ga wannan wata na Afrilu.
A cewarsa, Easter, lokaci ne na sabonta rayuwa da kuma fata na gari, amma a bana, bikin ya zo cikin wani yanayi na yaki.
Sojojin Ukraine dai sun tabbatar cewa, rikicin ya kazance a yankin gabashin kasar bayan shugaba Volodymyr Zelensky ya ce, Rasha ta kaddamar da gagarumin farmakinta da aka dade ana dako a Donbas.
A wani labarin na dabanHukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da wata Cibiyar Bincike ta duniya wadda za ta mayar da hankali wajen nazari akan magugunan gargajiya a kasar India da zummar cin gajiyar bangaren ta hanyar hada su da kimiyar zamani.
Hukumar Lafiyar ta ce cin gajiyar wannan bangare zai bude wani sabon babi a hanyar kula da lafiya, yayin da aka tabbatar da cewar magungunan gargajiya na taka rawa wajen kula da lafiyar jama’a.
Shugaban Hukumar Lafiya Tedros Adhanom Gebreyesus da Firaministan India suka halarci bikin kaddamar shirin gina Cibiyar a Birnin Gujirat, yayin da akayi kiyasin cewar akalla kasha 80 na jama’ar duniya na amfani da magungunan gargajiya.