Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana matukar kaduwar sa da kashe fararen hula sama da 130 da Yan ta’adda suka yi a kasar Burkina Faso wanda shine mafi muni tun daga shekarar 2015.
Gwamnatin Burkina Faso tace Yan ta’addan da suka aikata kisan sun kai hari ne cikin dare inda suka cinna wuta a gidaje da kuma kasuwar kauyen Yagha dake ci cikin dare a kusa da iyakar Mali da Jamhuriyar Nijar.
Bayan Allah-wadai da kazamin harin Guterres ya bayyana muhimmancin taimakawa kasashen duniya yaki da tsatsauran ra’ayi.
Majalisar Dinkin Duniya karkashin jagorancin Guterres ta bayyana cikaken goyan bayan ta ga hukumomin Burkina Faso a shirin da suke yin a magance wannan barazanar da kuma tabbatar da zaman lafia a cikin kasar.
A wani labarin na daban k;uma akalla fararen hula Azbinawa 11 aka kashe kusa da garin Menaka da ke arewacin Mali da ke fama da rikici, kamar yadda kungiyar dakarun kawance da ke goyon bayan gwamnati ta sanar a jiya Asabar.
Kungiyar ta ce wasu mahara da ba a shaida sub a ne suka kai hari a garin Agharangabo, inda suka aikata ta’asa.
Agharangabo da Menaka na daga cikin makeken yankin da aka amannar cewa gwamnati ba ta da iko a kan su kasar ta Mali, sakamAkon cewa su na karkashin ikon mayaka masu ikirarin jihadi.
Tun a shekarar 2021 ne yankin ke fama da hare hare daga mayaka masu ikirarin jihadi, da kuma munanan rikice rikice tsakanin al’umomi dabam dabam da ke zaune a yankin.
Rahotanni sun ce maharani sun yi awon gaba da dabbobin mutane 11 da suka kashe.
Kasashan afirka na fama da matsalolin tsaro sakamakon kutsen kasashen ketare a harkokin gudanarwar kasashen masu ma’adanai da tattalin arziki amma manyan kasashen duniya suna handamewa a lokaci guda suna talauta talakaawan kasashen yadda ba zasu iya samun wadataccen ilimi gami da wayewar da zasu kwaci kansu daga hannun manyan kasashen na duniya ba.