Guteress Zai Ziyarci Rasha A Wannan Talata.
Yau Talata ne ake sa ran babban sakataren MDD, Antonio Guteres, zai kai ziyara birnin Moscow.
Wannan ziyara a cewar sanarwar da ofishin MDD, ya fitar na da zummar tattaunawa da mahukuntan Rasha a wani yunkuri na kawo karshen yakin da Moscow ta kaddamar kan Ukraine.
Kafin ya ziyarci kasar ta Rasha, Mista Guteress, ya yada zango a birnin Ankara na kasar Turkiyya, inda ya gana da shugaba Recep Teyyeb Erdogan, wanda ya bayyana anniyarsa ta sasanta rikicin na Ukraine, da kuma batutuwan da suka shafi ayyukan jin kai.
Haka kuma babban sakataren na MDD, zai isa birnin Kiev, na Ukraine a ranar Alhamis, inda zai gaba da shugaba Volodymyr Zelensky, duk da dai a yunkurin kawo karshen yakin.
A yau dai shiga kwana na 61 na matakin sojin da kasar Rasha ta ce ta dauka kan Ukraine.
RAED MORE : Sojojin Isra’ila sun harbe wani matashi Bafalasdine a sansanin Aqabat Jabr da ke Jericho.
Kuma tattaunawar da ake tsakanin bangarorin da nufin kawo karshen yakin ta gaza har kawo yanzu.
Kimanin mutane miliyan 5,2 ne suka tserewa rikicin na Ukraine a cewar MDD.
READ MORE : Iran; Batun Falastinu Shi Ne Mafi Muhimmanci Ga Duniyar Musulmi.