Gwamnatin mulkin sojin da ta karbe mulki a kasar Guinea da ke yammacin Afirka ta kaddamar da wani “daftari” da ta ce za ta yi amfani da shi wajen mayar da mulkin kasar ga farar hula.
In ba a mance ba, a ranar 5 ga watan Satumba ne dakarun da ke karkashin jagorancin Kanar Mamady Doumbouya suka kama shugaba Alpha Conde mai shekaru 83 a duniya, bayn sun sun kifar da gwamnatin sa.
Yayin da Jakadan kasar Guinea a Majalisar Dinkin Duniya ya shaidawa taron Majalisar cewa, za a gudanar da gyare gyare kan kundin zaben kasar tare da rubuta sabon kundin tsarin mulki gabanin sabon zaben.
majalisar mai da mulki ga farar hular ta CNT mai kunshe da mambobi 81 da aka zabo daga jam’iyyun siyasa, kungiyoyin farar hula, kungiyoyin kwadago, masu daukar ma’aikata, jami’an tsaro da sauran hukumomi, za a dorawa alhakin tsara sabon kundin tsarin mulkin kasar.
A wani labarin na daban kuma Kafar talabijin din Rasha ta watsa faifan bidiyo na wasu ‘yan Britaniya da aka kama suna taya Ukraine yaki, inda suke bukatar Firayim Minista Boris Johnson ya shiga tattaunawa da Rasha don a sako su.
A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Biritaniya ta fitar, ‘yan uwan Pinner sun tabbatar da cewa sojojin Rasha suna tsare da mutanen biyu.
Sanarwar ta kara da cewa iyalan mutanen biyu suna aiki tare da ma’aikatar don tabbatar da ‘yancinsu yayin da ake amfani da yarjejeniyar Geneva da ta shafi fursunonin yaki.
Dama dai ita kanta Ukraine ta watsa wani video na attajirin, akan a yi musanyar sa ta hanyar kwashe fararen hula da sojoji daga birnin Mariupol da Rasha ta yi wa kawanya.
A baya dai fadar Kremlin ta yi watsi da ra’ayin musanya shi da ‘yan kasar Ukraine da Rasha ke tsare da su, yayinda Zelensky ya dage akan hakan.
Ukraine dai na zargin makusancin na Putin da cin amanar kasa da yunkurin satar albarkatun kasa daga Crimea da Rasha ta mamaye da kuma mika sirrin sojojin Ukraine ga Moscow.