Gwamnatin mulkin sojan Guinea Conakry ta ce hambararren shugaban kasar Alpha Conde ya samu yanci daga tsare shin da ta yi a baya, inda ta ce a yanzu, tsohon shugaban yana iya karbar baki.
Sai dai Jam’iyyar tsohon shugaban ta RPG, ta musanta cewar jagoran na ta ya samu ‘yanci kamar yadda sojojin suka bayyana, inda ta bukaci a bashi cikakken ‘yancinsa ba tare da wani sharadi ba.
Domin tabbatar da matsayin na ta, jam’iyyar ta RPG, ta dakatar da halartar taron sulhu na kasa da gwamnatin mulkin sojan Guinea ta shirya domin nuna rashin amincewa da matakin sojojin kasar.
Mai shekaru 84, Alpha Conde ya zama zababben shugaban kasar Guinea na farko ta hanyar dimokuradiyya a shekara ta 2010, kafin daga bisani sojoji su yi masa juyin mulki a shekarar da ta gabata, suka kuma maye gurbinsa da Kanar Mamady Doumbouya.
A wani labarin na daban ana fargabar cewar akalla mutane sama da 100 suka mutu sakamakon wata gobarar da ta tashi a wajen tace danyan man fetur ba bisa ka’ida ba akan iyakokin Jihohin Imo da Rivers da ke Najeriya.
Sai dai mai magana da yawun ‘Yan Sandan Jihar Rivers Grace Iringe-Koko tace yankin ba a cikin Jihar Rivers yake ba, inda ta kara da cewar yana Jihar Imo ne.
Jaridar tace Fyneface wanda ya gabatar mata da wasu hotunan hadarin da babu kyaun gani, yace bayan mutanen da suka kone kurmus, wasu motocin da suke dakon a zuba musu man satar suma sun kone kurmus.
Ko a makon jiya sanda aka samu irin wannan hadari a karamar hukumar Rumuekpe Emohua inda mutane sama ad 30 suka mutu cikin su harda yara, abinda gwamnatin Jihar Rivers ta danganta shi da fashewaer gas da satar man.
Jihohin Rivers da Imo na daga cikin wadanda ke fama da matsalar fasa bututun mai ana sata da kuma masu tace man a haramtattun matata.
A farkon shekarar nan Gwamnan Jihar Rivers Nyesom Wike ya kaddamar da samame akan barayin man da zummar dakile ayyukan su saboda abinda ya kira zagon kasa da matakin nasu ke yiwa tattalin arzikin Najeriya.