Kamar yadda Iqna ta ruwaito; Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na Shafaq ya bayar da rahoton cewa, ma’aikatar kula da harkokin addinin muslunci, da yada farfaganda da jagoranci ta kasar Saudiyya tare da hadin gwiwar sakatariyar harkokin addini ta kasar Guinea Conakry ne ke gudanar da wannan gasa.
A mataki na karshe na wannan gasa da ake gudanarwa a bangarori biyu maza da mata, akwai ‘yan takara 250 da suka fafata a fannoni 8.
An fara bikin bude wannan gasa ne a ranar Laraba 29 ga watan Maris inda aka gabatar da karatun ayoyin kur’ani da kuma jawabin “Sheikh Kermova Javara”, ministan harkokin addini na kasar Guinea-Konagri, da “Dansa Koroma” Shugaban majalisar dokokin kasar Guinea-Konagri, “Fahad Al-Rashidi”, jakadan Saudiyya a wannan kasa, “Sheikh Wahid Mojarabi”, darektan kula da harkokin addini na Jamhuriyar Senegal da jakadun wasu kasashen Larabawa da na Musulunci. suna daga cikin wadanda suka halarci wannan biki.
A ranar 15 ga watan Ramadan ne za a gudanar da bikin rufe wannan gasa tare da bayyana wadanda suka yi nasara.