Hotuna masu dauke da Isara’iliyawa suna tserewa, kashe masu tsaron iyakokin Isra’ila gami da dibar ganimar motocin yaki gami da sojojin Isra’ila da suke tserewa sanye da kayan gida na nuna yadda harin guguwar aqsa ya zo wa yahudawan Isra’ila a yanayi na bazata.
Watan Oktoba na zaman tuni ga Falasdinawa da kuma Isra’iliyawa na yakin da ya faru a shekarar 1973, lokacin da MIsra da Siriya suka fakaici Isra’iliyawa a lokacin da suke hutun idi kuma suka musu biji biji.
A safiyar yau Falasdinawa a wani hari tsararre ( Guguwar Aqsa) kuma wanda akayi shi bisa tsari suka tsallaka iyakar Isra’ila kuma a kasa da rabin awa suka cilla rokoki dubu 5.
Wanna hari na ba zata ya sanya gwamantin Isra’ila da ma shugaban kasar Ntanyaho cikin yanayin da ake ganin suna da rauni ta bangaren samun bayanai da kuma yanayi na rashin tsaro.
Amma sai dai dalilin da ya haddasa wannan hari shugaban dakarun kassam wadanda suka kai wannan hari ya tabbatar da cewa: “An kaiwa mata masu i’itikafi hari a masallacin Al-aqsa kuma an shiga hurumin wannan masallachi tattare da cewa anyi musu gargadi a tun tuni, daruruwan Falasdinawa ne suka rasa rayukan su, wasu kuma suka mutu sakamakon zaluncin Isra’iliyawa”
Abinda zai biyo baya ya danganta da matakin da Isra’ila zata dauka amma abinda ya fito fili shine, musulmi sun samu nasara zuwa yanzu.
Kwana hudu kenan ana fafatawa, zuwa yanzu Isra’ila ta kai hare haren ba sani ba sabo inda ta kashe fararen hula daruruwa tattare da masu yawa wadanda suka ji munanan raunuka bayan gidaje da aka rugurguje.