Gudanar Da Zaben Raba Gardama A Kasar Falasdinu Ita Ce Mafita A Riki Kasar Da Aka Mamaye-Abdullahiyan.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Amir Hussain Abdullayin ya bayyana cewa hanyar warware rikicin Falasdinu ita ce gudanar da zaben raba gardama wanda dukkan ‘yan asalin kasar Falasdinu, musulmi kirista da kuma yahudawa, na ciki da wajen kasar zasu gudanar.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Abdullahiyan yana fadar haka a jawabin da ya gabatar a taron hadin kan al-ummar musulmi na yankin gabas ta tsakiya wanda aka gudanar a garin Sanandaj na kasar Iran a ranar Laraba.
Ministan ya bayyana cewa wannan shi ne ra’ayin jagoran juyin juya halin musulunci Ayatullahi Imam Aliyul Khaminaee tun shekara 20 da suka gabata.
Ministan yace JMI ta gabatar da wannan shawarar ga MDD kuma ta bukaci a kafa asusun na musamman don tara kudaden lissafa falasdinawa na asali a cikin da wajen kasar a ko ina suke a duniya, sannan don gudanar da zaben raba gardamar.
Daga karshe Amir-Abdollahian ya kammala da cewa zababbubun wakilan wadannan Falasdinawa ne zasu fayyace makomar kasar ta Falasdinu.
Daga karshe minisyan ya bayyana samar da huldar jakadanci tsakanin wasu kasashen Larabawa da HKI ha’inci ne ga al-ummar Falasdinawa.