Da yammacin yau laraba 3 ga watan janairu 2024 da karfe 2: 50pm a hanyar makabartar Golzar shuhada’a dake garin kerman aka jiyo wata karar abin fashewa a cikin jama’a wanda hakan ya sanya mutane cikin razani kuma wasu suka ji raunuka sakamakon turereniya.
A halin yanzu jami’an agajin gaggawa na ta kokarin ceto rayuwar mutane amma an tabbatar da shahadar mutane 25 yayin da wasu arba’in suka ji raunuka.
Dan jaridar dake wakiltar gidan jarida na Tasnim ya rubuta cewa:
‘Yan mintuna da suka gabata a hanyar makabartar Golzar Shuhada aka jiyo kara mai ban mamaki inda bayan nan ma’aikatan bada taimakon gaggawa suka tafi wajen domin ceton rayukan al’umma.
Kamar yadda jaridar Tasnim ta tabbatar wannna abin fashewar ya fashe ne a kusa da masallachin Sahibuzzaman amma har lokacn hada wannan rahoto ba’a samu cikakken bayani dangane da lamarin ba.
Mutane sun watse daga wajen kuma jami’ai sun isa wajen domin daidaita al’amura.
Wasu daga cikin wadanda suke wajen lokacin da lamarin ya faru sun tabbatar da cewa, tukunyar gas ce ta fashe kuma itace tayi sanadiyyar faruwar lamarin amma zuwa yanzu babu wani bayani daga bangaren jami’an da abin ya shafa.
Motocin asibiti da dama sun halarci wajen domin ba da tallafin gaggawa ko za’a samu mai bukatar hakan.
A halin yanzu jami’an tsaro sun hana mutane bi ta wannan hanyar ta Golzar Shuhada kuma ana kan bincikar lamarin domin tabbatar da asalin dalilin aukuwar lamarin.
A rahoton da shugaban agajin gaggawa na kerman ya tabbatar da smaun mutane 15 da sukaji raunuka a dalilin wannan lamari da ya faru.
Zuwa yanzu majiyoyi masu tushe sun tabbatar da rasuwar mutane 103 da kuma 201 wadanda sukaji raunuka, an kuma sanar da Alhamis matsayin ranar makoki a gabadayan Kasar Iran.