Kafafen yada labarai a kasar Lebanon sun bada labarin mutuwar mutane 12 da kuma raunata akalla mutanen 20 sanadiyyar gobara wacce ta tashi kusa da rumbun ajiye makamai na kungiyar Hamas a sansanin ‘yan gudun hijirar Falasdinawa da ke “Buj Shumali’ a birnin na kudancin kasar Lebanon a jiya Jumma’a.
Labarin ya kara da cewa da farko gobarar ta tashi a ma’ajiyar gasoline sannan ta yadu zuwa ga rumbun ajiyar makamai na kungiyar Hamas dake kusa da sansanin ‘yan gudun hijirar ta ‘Buj Shomali’. Gobarar har’ila yau ta kona wani masallaci kuda da wurin. Mai yuwa yawanda suka rasa rayukansu ya karu don munin da wasu wadanda suka ji rauni suke ciki. Tuni dai jami’an kwanakwana na kungiyoyin Hizbulla da Amal sun kashe gobarar. Har’ila yau jami’an tsaro kasar sun je sansanin yan gudun hijirar don tabbatar da tsaro a wurin.
Sai kuma mai gabatar da kara a ma’aikatar shari’a na kasar Lebanon ya bukaci jami’an tsaron kasar su gudanar da bincike don gano musabbin gobarar. An kafa sansanin yan gudun hujiran falasdiawa ta ‘’Burj Shomali’ ne a shekara ta 1955 kusa da garin Sur, kuma daya ne daga cikin sansanonin ‘yan gudun hijirar Falasdinawa 12 inda fiye da Falasdinawa 400,000 suke samun mafaka a cikinsu.