Girka; Wata Babbar Kotu A Birnin Athen Ta Yanke Hukuncin Mayarwa Iran Danyen Man Fetur Gabda 700,000.
Wata babbar kotu a kasar Girka ta yanke hukuncin cewa a mayarwa kasar Iran danyen man fetur gan 700,000 wanda gwamnatin kasar Amurka ta sace tare da taimakon kasar Girka a cikin watan Mayun wannan shekara.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa a ranar 25 ga watan Mayun da ya gabata ne gwamnatin kasar Amurka tare da taimakon gwamnatin kasar Girka ta kwace jirgen ruwan mallakin gwamnatin kasar Rasha mai suna Lona, amma dauke da danyen man fetur na kasar Iran gangan 700,000.
Sai kuma a ranar 7 ga watan yuni gwamnatin kasar Iran ta shigar da kara a gaban wata babban kotu a birnin Athen, wacce da farko ta bata hukuncin wata karaman kotu wacce ta bada umurnin a kwace jirgin sannan daga karshe ta yanke hukuncin a mayarwa kasar Iran danyen man fetur wanda Amurka ta sace ta tafi da shi tare da taimakom gwamnatin girka.
Gwamnatin kasar Girka ta tabbatar da labarin amma bata yi karin bayani kan yadda za’a mayarwa Iran danyen man fetur din ba, ganin cewa Amurka ta sace man ta tafi da shi Amurka.