Girgizar Kasa Ta Yi Ajalin Mutum 280 A Afganistan.
Rahotanni daga Afganistan na cewa kimanin mutum 280 ne suka rasa rayukansu a wata mummunar girgiza kasa data auku a gabashin kasar.
Girgizar mai karfin maki 6.1 ta afku a nisan kilomita 44 daga birnin Khost da ke kusa da iyakar Pakistan, in ji hukumar binciken yanayin kasa ta Amurka.
Ko baya ga wadanda suka rasun da akwai wasu daruruwa da suka jikkata sakamakon girgizar kasar da ta afku a yankin kudu maso gabashin kasar har zuwa wasu yankuna na makwabciyarta Pakistan, in ji hukumar kula da bala’o’i ta kasar.
Shugaban ma’aikatar kula da bala’o’i ta gwamnatin Taliban, Mohammad Nassim Haqqani, ya ce akasarin wadanda suka mutu sun kasance a lardin Paktika.
READ MORE : Morocco;’Yan Jarida Sun Bayyana Yarjejeniyar Kafofin Yada Labarai Da Isra’ila A Matsayin Tsokana.
Wannan bala’in dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasar Afganistan ke fama da matsananciyar matsalar tattalin arziki tun bayan da kungiyar Taliban ta karbe iko a watan Agusta, bayan da dakarun kasa da kasa karkashin jagorancin Amurka suka janye bayan shafe shekaru ashirin a kasar ta Afganistan.
READ MORE ; Iran Ta Yi Watsi Da Rahoton Guterres Kan Take Hakkin Bil’adama A Kasar.