Akalla mutane 2,445 ne suka mutu sakamakon wata girgizar kasa mafi muni da ta afku a kasar Afganistan da ke fama da tsaunuka. in ji gwamnatin kasar a ranar Lahadi.
Hukumar Kula da Yanayin Kasa ta Amurka (USGS) ta ce, girgizar kasar da ta afku a ranar Asabar a yammacin kasar, ta shafe kusan kilomita 35 daga arewa maso yammacin birnin Herat. Girgizar kasar ta kai girman maki 6.3.
Janan Sayeeq, kakakin ma’aikatar kula da bala’ai, ya bayyana a wani sako da ya aikewa kafafen yada labarai na kasa da kasa cewa, adadin wadanda suka mutu ya kai 2,445, adadin wadanda suka jikkata kuma ya haura 2,000, da farko ya ce, mutane 9,240 ne suka jikkata.
Sayeeq ya kuma ce, girgizar kasar ta lalata gidaje 1,320.
A wani labarin na daban sarkin Kudan, Malam Muhammad Bello Haladu ya taya mai martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli murnar cika shekara 3 a kan karagar mulkin Masarautar Zazzau da ke Jihar Kaduna.
Sanarwar da ta fito daga Wakilin Yada Labarun Masarautar Kudan, Malam Yusuf Ibrahim Kudan, ta bayyana cewa, sarkin, Muhammad Bello Haladu ya bayyana cewa kasancewar mai martaba Ambasada Bamalli a kan karagar mulkin Zazzau ta kawo ci gaba mai dimbin yawa ba kawai a masarautar ba har da Jihar Kaduna da ma kasa baki daya.
Ya yi addu’ar Allah ya kara yaukaka dangantaka mai dorewa tsakanin Masarautar Zazzau da sauran masarautun da ke fadin kasar nan domin samun ci gaba mai ma’ana.
Sarkin na Kudan ya kuma bayyana kudirinsa na ci gaba da ba da goyon baya ga hakiminsa da sauran hakimai na Masarautar Zazzau baki daya.
Daga karshe Muhammad Bello ya roki al’ummar Masarautar Kudan su ci gaba da zama lafiya da juna domin samun ci gaba ba tare da la’akari da bambancin kabila, addini ko siyasa ba
Source LEADERSHIPHAUSA