A cewar Mahukuntan girgizar kasar ta shafi wani yanki na babban birnin lardin Mashhad da ke gab da iyakar Iran da Turkmenistan, birnin na biyu mafi girma a kasar.
Kungiyar agaji ta Red Cresent ta ce jami’an ta na cikin shirin ko ta kwana don tunkarar duk wani kalubale da girgizar kasar ka iya haifarwa a yankin.
A wani labarin na daban hukumomin kasar Haiti sun ce adadin mutanen da girgizar kasar da aka samu makon jiya ta kashe ya karu zuwa dubu 2 da 207.
Gwamnatin Haiti ta ce akalla mutane dubu 600 girgizar kasar ta makon jiya ta shafa.
Wata sabuwar barazana kuma da ma’aikatan agaji ke fuskanta a ita ce harin da gungun mutane zauna gari banza ke kai musu, abinda ya haifar da cikas ga aikin raba kayan agaji ga wadanda suka tsira daga iftila’in girgizar kasar.