Iran ta mayar da martani dangane da rahoton da kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya fitar kan batun kare hakkin bil adama.
A cikin bayanin da ya fitar, wakilin Iran a hukumomin kasa da kasa Kazim Gharib Abadi ya bayyana cewa, rahoton majalisar dinkin duniya kan batun hakkin bil adama a kasarsa batu ne siyasa, domin kuwa daftarin kudri na siyasa da wasu kasashe suka mika, domin cimma manufofinsu an siyasa a kan kasar ta Iran.
Ya ci gaba da cewa, abin ban takaici ne yadda bangarorin majalisar dinkin duniya suka zama wajen aiwatar da manufofin siyasar wasu kasashe, maimakon aiwatar da ka’idoji da aka kafa majalisar akansu tun daga farko.
Gharib Abadi ya ce, kasashen da suka gabatar da wannan kudirin sun fi kowa sanin inda ake take hakkin bil adama, amma kuma suka yi shiru da bakinsu, saboda babu maslahar siyasa a gare su idan suka yi hakan.
Ya kara da cewa, bil hasali ma kasashen da ke da’awar kare hakkin bil adama a duniya, su ne suka fi kowa cin zarafin dan adam da zubar jininsa da take hakkokinsa a duniya.